ZAZZABIN LASSA: Mutum 691 sun kamu, 132 sun mutu a Najeriya daga Janairu-Afrilu

Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Afrilun 2022 zazzabin lassa ta yi ajalin mutum 132 a kasar nan.

Mamora ya ce sakamakon gwajin cutar da aka gudanar a jikin mutum 3,746 ya nuna cewa mutum 691 ne suka kamu da cutar a jihohi 23 a kasar nan.

Ya ce bana an samu karin kashi 19.1% a yaduwar cutar a kasar nan.

Mamora ya fadi haka ne a taron da kwamitin dakile yaduwar cutar korona PSC ta yi da manema labarai a Abuja ranar Litini.

Idan ba a manta ba hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa a mako na 11 wanda ya fara daga ranar 14 zuwa 20 ga Maris 2022 mutum 29 sun kara kamuwa da cutar sannan mutum shida sun mutu a jihohi 11 a kasar nan.

Hukumar ta ce jihohin Ondo, Edo, Bauchi, Taraba, Kogi, Enugu, Ebonyi, Nasarawa, Oyo, Filato da Anambra na cikin jihohin da aka gano cutar.
Sannan jihohin Ondo, Bauchi- da Edo na cikin jihohin da suka fi fama da yaduwar cutar.

Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da Zazzabin Lassa

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.