Fitilar Wasannin Olympic Zata Cigaba Da Ci A Kusa Da Garin Louvre Yayin Wasannin Birnin Paris -A Cewar Wata Majiya

Wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar, an shirya cewar fitilar wasannin Olympic zata cigaba da ci a Lambun Tuileries dake gidan adana kayan tarihi na Louvre tsawon lokacin da za’a dauka ana gudanar da wasannin birnin Paris tsakanin watannin Yuli da Agusta masu zuwa