Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga majalisa, ya kama aikin APC gadan-gadan

Sanata Abdullahi Adamu ya aika da wasikar yin murabus daga majalisar dattawa.
Shugaban Majalisar, Ahmed Lawan ne ya karanta wasikar inda ya ce Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus ne domin ya fuskanci aikin shugabancin jam’iyyar APC wanda ya ke shugabanta.
Haka shima Abubakar Kyari dake wakiltar Barno ta Arewa a Majalisar Dattawan ya yi murabus daga majalisar.
An zabi Kyari mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa.
Bisa wannan sanarwa, shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan zai aika wa hukumar Zabe domin a gudanar da zabe a kujerun sanatocin biyu.