Wani ‘Dan Najeriya Na Kokarin Kafa Tarihi A Wasan Chess Don Neman Ilmantar Da Yara Miliyan 1 A Afirka

Wani zakaran dara na wasan Chess, ‘dan Najeriya kuma mai fafutukar koyar da ilimin yara yana kokarin buga dara na tsawon sa’o’i 58 ba tare da tsayawa ba a dandalin Times Square na birnin New York domin karya tarihin duniya na tsawon wasan chess mafi dadewa.