Ƴan bindiga sun kashe dagacin Maisamari a yayin da yake sallar Isha’i bayan buɗa baki

Ƴan bindiga sun kashe dagacin garin Maisamari Sufiyanu dake karamar hukumar Sardauna, Jihar Taraba.
Mazauna garin Maisamari sun shaida cewa ƴan bindigan sun kawo hari masallacin a daidai dagacin yan ciki yana sallar Isha’i tare da jama’a.
Wannan hari ya zo kwanaki biyu kacal bayan ƴan bindiga sun kai hari kananan hukumomin Gassol da Karim Lamido dake jihar.
Jihar Taraba na daga cikin jihohin da suka yi ƙaurin suna a yankin Arewa Maso Gabas da hare-haren ƴan bindiga ya yi tsanani, ma samman garkuwa da mutane.