ZAƁEN GWAMNAN JIGAWA: Namadin APC ya natsar da Lamidon PDP a Jigawa, ya lallasa shi da kuri’u 618,449

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Umar Namadi na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Jigawa.
Jami’in mai kula da zaben Farfesa Umar Zaiyan na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi ne ya sanar da sakamakon zaben ranar Lahadi a Dutse.
Zaiyan ya ce Namadi ya samu kuri’u 618,449 inda ya doke abokin hamayyarsa, Mustapha Sule Lamido wanda ya samu kuri’u 368,726.
Ya ce: “Ni Farfesa Umar Zaiyan na tabbatar da cewa Umar Namadi na jam’iyyar APC, bayan ya cika sharuddan doka na ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jigawa.”
A cewarsa, mutane miliyan 1.07 ne aka tantance su a zaben na ranar 18 ga watan Maris da kuri’u miliyan 1.05, daga cikin kuri’u miliyan 1.03 suka yi zaben.
Ya doke Malam Aminu Ringim na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) wanda ya samu kuri’u 37,156.
A baya dai PDP ta yi kira ga jami’in da ya dawo ya bayyana wani sashe na zaben a matsayin wanda bai kammala ba.