KURUNKUS: Abba Gida-Gida ya doke ɗan takaran Uban Abba, Gawuna na APC da kuri’u sama da miliyan ɗaya a Zaɓen gwamnan Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Da yake sanar da sakamakon zaben a ranar Litinin a Kano, Baturen Zabe Farfesa Doko Ibrahim, mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya ce Yusuf ya samu kuri’u 1,019,602 da ya lashe zaben.
Ibrahim ya ce Yusuf ya doke abokin hamayyarsa kuma mataimakin gwamnan jihar mai ci Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 892,705.
Ya ce: “Ni Farfesa Doko Ibrahim na bayyana cewa ‘yan takara 18 ne suka fafata a zaben.
“Bayan cika sharuddan doka kuma Abba Yusuf ya samu mafi yawan kuri’u, da hakan ya sa shi ne ya lashe zaben kuma zaɓaɓɓen gwamnan Kano.