ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: An kashe shugaban PDP bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a rumfar zaɓen sa

An bayyana rasuwar Shugaban PDP na Ƙaramar Hukumar Ezza ta Arewa a Jihar Ebonyi, bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a ranar zaɓen gwamna.
Marigayin mai suna Peter Nweke, ya mutu sakamakon munanan raunuka da aka ji masa, lokacin da wasu ‘yan jagaliya su ka riƙa lallasa shi a rumfar zaɓen sa, a wurin jefa ƙuri’a.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar wa manema labarai rasuwar jigon PDP ɗin a ranar Litinin.
Ya ce an garzaya da shi asibiti inda likitoci su ka tabbatar da cewa ya rigaya ya mutu.
‘Yan sanda sun ce sun fara binciken waɗanda su ka yi kisan domin a kamo su a hukunta su.
Ɗan uwan mamacin mai suna Samson Nweke, ya tabbatar da rasuwar jigon na PDP, ya ƙara da cewa maharan a kan babura biyu su ka je, kuma kowa saɓe da bindiga ƙirar AK47.
Sannan kuma ya ce ko kafin ranar zaɓe sai da mamacin ya same shi har gida ya gargaɗe shi cewa ya yi kaffa-kaffa da ran sa, domin ‘yan wata jam’iyya sun bada ‘kwangilar’ kashe shi.