ZAƁEN 2023: Babu dalilin da zai sa PDP ta damƙa takarar shugaban ƙasa ga ‘yan kudu -Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso ya nuna rashin yardar sa ga masu neman jam’iyyar PDP ta miƙa takarar shugaban ƙasa ga kudancin ƙasar nan.

Kwankwaso ya bayyana wannan ra’ayi ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels, a ranar Lahadi, inda ya bayyana wannan matsaya ta sa.

Kwankwaso ya la’anci matsayar gwamnonin kudu a cikin watan Yuli, 2021, inda su ka kafe su ka ce sai dai PDP ta fito da ɗan takara a zaɓen 2023 na shugabancin ƙasar nan.

Labaran da ke yawo a gari na cewa matsalar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ta dabaibaye jam’iyyar APC da PDP, saboda ta kai har su biyun na tunanin janye tsarin karɓa-karɓa, a ce duk mai iyawa ya fito takara kawai.

Da ya ke magana a kan ji-ta-ji-ta da ake watsawa cewa zai koma APC, Kwankwaso ya ce ƙarya ce, ba gaskiya ba ne. Kuma ya na cikin PDP, sannan zai taimaka jam’iyyar ta lashe zaɓen 2023.

Ya ce ji-ta-ji-tar zai koma takara ta samo asali ne daga wurin taron jam’iyya wanda aka shirya a Kaduna, cikin shekarar 2021.

“Yanzu haka da na ke maganar nan da kai, ba ni da wata aniyar barin PDP wai na koma APC, ko ma wata jam’iyya.

“Kawai surutan sun taso daga taron PDP na Kaduna a cikin watan Afrilu, inda na yi ƙorafin cewa Ni da jihar Kano ba a yi mana adalci ba a wurin taron.

“To na yi imani cewa daga can ne maganganun suka taso. Mutane dama sun yi ta cewa mu fice daga PDP mu koma APC ko wata jam’iyyar daban.

Da aka tambaye shi batun rikicin sa da Ganduje, Kwankwaso ya riƙa lissafo irin gudunmawar da ya yi wa Ganduje a tarihin siyasar sa.

Ya ce tun da Ganduje ya hau mulki cikin 2015, bai kai masa ziyara ba, sai fa kwanan nan da ya je yi masa ta’aziyyar yayan sa.