KORONA: Mutum 537 sun kamu, mutum 6 sun mutu ranar Lahadi a Najeriya

Sakamakon gwajin cutar korona da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa mutum 537 sun kamu da korona sannan mutum 6 sun mutu bayan sun kamu da cutar a jihohi 7 da Abuja.

Alkaluman sakamakon cutar na ranar Asabar ya nuna cewa mutum 766 ne suka kamu da cutar sannan mutum 1 ya mutu a jihohi 12 da Abuja.

Zuwa yanzu mutum 248,312 ne suka kamu, an sallami mutum 218,997 sannan akwai mutum 26,238 dake dauke da cuta a jikinsu.

Cutar ta yi ajalin mutum 3,077 a Najeriya.

Yaduwar cutar

Legas – 97,054, Abuja-27,673, Rivers-15,672, Kaduna-11,010, Filato-10,209, Oyo-10,083, Edo-7,576, Ogun-5,759, Kano-4,828, Akwa-ibom-4,566, Ondo-4,998, Kwara-4,015, Delta-4,446, Osun-3,123, Enugu-2,824, Nasarawa-2,648, Gombe-2,695,

Katsina-2,367, Ebonyi-2,048, Anambra-2,424, Abia-2,144, Imo-2335, Bauchi-1,896, Ekiti-1,955, Benue-2,109, Barno-1,577, Adamawa-1,136, Taraba-1,254, Bayelsa-1,303, Niger-1,077, Sokoto-810, Jigawa-642, Yobe-501, Cross-Rivers-662, Kebbi-458, Zamfara-348, da Kogi-5.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa nau’in Omicron na jikkita mutane idan suka kamu kuma tana gaggawar aika wa da mutum lahira idan ba a shawo kanta da wuri ba.

Shugaban hukumar Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka ranar Alhamis a taron da ya yi da manema labarai kan yaduwar cutar korona inda ya gargaɗi mutane cewa bai kamata a rika sakwasakwa da cutar ba.

Ghebreyesus ya ce nau’in Omicron na yaduwa kamar walkiya sannan a yanzu haka asibitoci a duniya sun fara samun daruruwan mutane da ake kai musu kuma har an fara samu karancin jami’an lafiya