KURUNKUS: Na zo fadar Buhari in sanar masa ‘zan yi takarar shugabancin Najeriya a 2023’ – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC kuma jigo a tafiyar shugaba Buhari tun daga 2015 zuwa yanzu Bola Tinubu ya bayyana wa manema labarai a fadar gwamnati cewa ya garzayo Aso Rock ne domin ya shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yana da Burin yin takara a 2023.

Wannan bayani ya biyo bayan ganawar sirri da yayi ne da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati ranar Litinin.

” Na sara da Buhari abinda shi ab-burina wato takarar shugabancin Najeriya, sai dai har yanzu ina ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma sauran al’umma. Nan ba da dadewa ba zan sanarwa wa ‘yan Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu na daga cikin wadanda tun bayan darewa kujerar shugabancin shugaba Buhari ake raderadin shine zai gaji shi idan wa’adin mulkin sa ya cika a 2023.

Tuni har magoya bayan sa sun fara Kamfen daya bayan daya a wasu sassan jihohin kasar nan ciuki har da jihar Kano, wanda a kwanakin baya aka rika raba buhunan shinkafa da wake domin tallata jagorarn APC din.