Yara kanana na batar dabo a Jigawa – Gwamna Badaru

Gwamna Muhammad Badaru na Jihar Jigawa a ranar Alhamis yayi Kira ga Iyaye da al’umma da su gaugauta sanar da hukumomi a Jihar idan suka gani wane bakon fuska dake shawagi a yankunansu.

Badaru yayi kira ne bayan samun rahotannin yadda yara kanana ke batar dabo a fadin Jihar ta Jigawa a wannan kwanaki na kurkusa.

Kakakin gwamna Badaru, Habibu Kila, a cikin wata sanarwa, yace gwamnan yayi kira ga Iyaye da sauran Jama’a dasu farga, kuma su sa wa ya’yan idanu su rika sanin zirgazirgar su da hana su galantoyi da gararambar babu gaira babu dalili domin kada su fada hannun muggan mutane.

Sanarwar na gwamnati bata bayyana yawan yaran da ake nema ba, amma binciken wakilinmu ya gano cewa a kalla Yara biyar sun bata a cikin makonnin da suka gabata a fadin Jihar.

Shi ma a nasu bangaren, Kakakin ‘Yan Sandar Jigawa, Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar bace-bacen yara a Jihar amma yace ‘Yan Sandar na tattara alkaluman yawan adadin yaran da suka baci zuwa yanzu.

Gwamna Badaru ya hori iyaya su dauki mataki domin girmar yawan korafi da ake kawowa kan batan yara.

Badaru yace gwannati tsaye kan tabbatar da tsaro a Jihar, kuma ta dukufa wajen walwalar al’ummanta kuma zata cigaba da samar da tsaro a fadin Jihar.

Gwamna Badaru yayi Kira ga Al’umma da masu ruwa da tsaki su tashi su taimaka wajen Kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar baki.