‘Yan tawayen Kamaru sun kutsa Taraba, sun kashe Basarake da mutum 10 a Takum

Wasu mahara da aka tabbatar cewa ‘yan tawayen Ambazonia ne daga tsallaken Kamaru, sun kutsa cikin Jihar Taraba, inda su ka kashe Sarkin garin Manga a Ƙaramar Hukumar Takum da kuma wasu mutum 10.

Waɗannan ‘yan tawaye dai su na neman ɓallewa ne daga Kamaru, domin ƙafa ƙasar da su ke kira Ambazonia, mai magana da harshen Turancin Ingila, ba Faressncin Faransa da Kamaru ke magana da shi ba.

A yau Alhamis ne Hadimin Gwamna Darius Ishaku msi suna Joseph Manga, ya shaida wa BBC Hausa cewa Sarkin Manga da aka kashe ɗin ɗan uwan sa ne. “Sun isa garin wajen 5:30 na asubahi, ta hanyar yin amfani da ƙananan kwale-kwale masu gudun tsiya.

“Su na isa suka riƙa harbe mutane kuma su na banka wa gidaje wuta.

“Bayan sun tafi, an nemi mutane da dama, maza da mata ba a gani ba. Ana tunanin sun yi garkuwa da su.”

Joseph Manga ya ce ba wannan ne karon farko da ‘yan tawayen Ambazonia su ka fara kai hari a garin Manga ba.

“Mun yi iyaka da su ta wannan ruwa. Daga can su ke tsallakowa suna hare-haren hana manoman mu yin noma ko girbe amfanin gonar da su ka yi a gonakin su.”

Manga ya ce a yanzu dai gwamnatin Najeriya ta tura jami’an tsaro a yankin.