Gwamnati ba za ta yi sakwa-sakwa wajen tilasta wa mutane su yi rigakafin korona ba – Boss Mustapha

Shugaban kwamitin korona na kasa PSC Boss Mustapha ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi sakwa-sakwa ba wajen tilasta mutane musamman ma’aikatan gwamnati su yi allurar rigakafin korona a kasar nan.

Mustapha ya fadi haka ne a taron da kwamitin ta yi da manema labarai a farkon wannan mako a Abuja.

Ya ce rahotanni sun nuna cewa korona ya ci gaba da yaduwa a wasu kasashen Turai saboda rashin yi wa mutane allurar rigakafin cutar.

“Mun kuma samu rahoton cewa cutar ya ci gaba da yaduwa a wasu kasashen da suka yi wa mutanen su allurar rigakafin korona. Sannan a nan Najeriya cutar na ci gaba da kisa.

“Idan ba a manta ba a kwanakin baya mun sanar cewa gwamnati za ta fara tilasta wa ma’aikatan gwamnati yin allurar rigakafin cutar a kasar nan daga ranar 1 ga Disemba.

Kiyaye dokar fita kasashen waje

Mustapha ya yi kira ga mutanen dake shirin fita zuwa kasashen waje da su tabbatar sun kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar da kasashen duniya suka saka.

Ya ce ya yi wannan kirane ganin yadda matafiya suke samun matsalolin wajen shiga wasu kasashe a dalilin rashin kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar da gwamnatocin kasashen suka saka.

Yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona.

Mustapha ya ce gwamnati ta kammala yin shiri domin ganin an fara yi wa mutane da dama allurar rigakafin korona a kasar nan.

Ya ce gwamnati ta samar da magungunan rigakafin korona da zai isa a yi wa mutum kashi 50% a kasar nan.

“Nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara yi wa mutane allura da maganin da zai taimaka wajen kare mutanen daka kamuwa da korona.