‘Yan Ta’adda Sun Kona Motocin Dakon Albasa Mallakar ‘Yan Nijar A Wani Jejin Burkina Faso

Shugabanin kungiyoyin manoman albasa  da masu fitar da ita kasashen ketare sun koka a game da babbar asarar da matsalolin tsaro ke haddasa wa wannan fanni inda ‘yan ta’addan Burkina Faso ke kona motoci dauke da lodin albasa akan hanyarsu ta zuwa Cote d’Ivoire da Ghana