Mutum sama da 4,000 sun kamu da zazzabin lassa a Najeriya – NCDC

Sakamakon yaduwar cutar zazzabin lassa da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta fitar ya nuna akwai mutum 4,338 da suka kamu da cutar a kasar nan zuwa yanzu.

Hukumar ta ce cutar ya ci gaba da yaduwa daga ranar 2 ga Afrilu 2023.

NCDC ta ce daga mako na daya zuwa mako 13 mutum 847 ne suka kamu sannan cutar ta Yi ajalin mutum 148.

A mako na 13 da ya fara daga ranar 27 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu an samu ragowar yawan mutanen dake dauke da cutar daga mutum 39 a mako 12 zuwa mutum 23.

Sannan a yawan mutanen da cutar ke kashewa an samu karuwa daga mutum biyu zuwa hudu.

Hukumar ta ce akalla mutum daya ya kamu da cutar a kananan hukumomi 99 dake jihohi 25 a kasar nan.

An samu kashi 72% na yaduwar cutar a jihohin Ondo, Edo da Bauchi.

A mako na 13 wani jami’in lafiya daya ya kamu da cutar.

Zazzabin lassa

Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.

Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.

Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.

Alamun cutar

Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.

Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.

Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.

Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.

Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.

Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.

Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.

Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.