‘Yan sandan Kaduna sun yi babban kamu tsakanin watannin Agusta zuwa Disamba

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta damƙe gaggan masu laifi har 25 tare da makamai tsakanin watan Agusta da Satumba.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Kaduna, Muhammad Jalige ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, a lokacin da ya ke wa manema labarai bajekolin masu laifin, a hedikwatar ‘yan sandan jihar, a Kaduna.

Ya ce an kama su ne bayan sun aikata muggan laifuka da su ka haɗa da fashi da makami, kisan kai, garkuwa da mutane, ayyukan ƙungiyoyin asiri, mallakar muggan makamai da sauran laifuka daban-daban.

Daga cikin waɗanda aka kama har da waɗanda su ka haɗa kai su ka dira gidan direban jirgin sama, kuma ɗan Sanata Bala Ibn Na-Allah, wato Abdulkareem Na-Allah, su ka kashe shi a cikin gidan sa.

Sun dira gidan sa cikin dare a ranar 26 Ga Agusta, su ka kashe shi, kuma su ka tsere da wasu kayayyakin sa, ciki kuwa har da motar sa.

Jalige ya ce an samu makamai samfuran bindigogi daban-daban a hannun masu aikata muggan laifukan, waɗanda yawanci duk sun amsa laifin su.

Ya ce da an gama bincike za a damƙa wa kotu su, domin hukunta su daidai da laifukan da su ka aikata.