Sojoji sun kubutar da jami’in su da ƴan bindiga suka sace a NDA

Rundunar soji ta ce ta ceto Manjo Datong, sojan da ƴan bindiga suka sace a harin da suka kai kwalejin koyon aikin soja ta NDA a Kaduna a watan da ya gabata.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a ta ce an ceto sojan ne bayan musayar wuta da ƴan bindiga tare da tarwatsa sansaninsu da suke tsare da jami’in sojan a yankin Afaka- Birnin Gwari.

  • Sojoji sun kubutar da jami’in su da ƴan bindiga suka sace a NDA
  • ‘Za mu kammala aikin hanyar Numan-Gombe zuwa ƙarshen watan Disamba’- Gwamnatin Tarayya

Sanarwar ta kuma ce ƴan bindiga da dama ne aka kashe a farmakin da sojojin suka kai tare da taimakon ƴan sanda a ranar Juma’a.

“Sojojin sun yi nasarar ceto jami’in sojan, ko da yake ya samu rauni amma an yi masa magani,” in ji sanarwar.

A ranar 24 ga watan Agusta ne ƴan bindiga suka abka makarantar sojoji ta NDA da ke Kaduna inda suka kashe sojoji biyu kuma suka sace ɗaya.

Harin dai ya girgiza ƴan Najeriya, kasancewar yadda ƴan fashin masu satar mutane da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya har suka shiga makarantar inda ba a taɓa zato za su iya abka wa.

An wallafa wannan Labari September 18, 2021 9:40 AM