‘Yan sandan jihar Adamawa sun kama mayu 21 da suka cinye wasu mutum 7 a ƙauyen Dasin Bwate

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane su 21 da ake zargi Mayu ne sun cinye kurwar wasu mutum 7 a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Aliyu Adamu ya fadi haka ne a taron da ya yi da manema labarai ranar Litini a garin Yola.

Adamu ya ce rundunar ta kama wadannan mutane a kauyen Dasin Bwate dake karamar hukumar Fufore.

Ya ce rundunar ta samu wannan nasara da sauran nasarorin irin haka a dalilin hada hannu da ta yi da sauran jami’an tsaron dake jihar da suka hada da mafarauta da ‘yan banga.

“Sauran nasarorin da rundunar ta samu sun hada da kama batagari guda 1,146 inda mutum 426 daga ciki an yanke musu hukunci a kotu sannan mutum 720 na jira kotu ta yanke musu hukunci.

“Hadin gwiwar da muka yi da sauran jami’an tsaro ya taimaka mana wajen kamo wadannan matsafa wato mayu su 21 da ake zargi su a da hannu a kisan mutum bakwai a kauyen Dasin Bwate.

Bayan haka Adamu ya ce rundunar ta kama wasu ‘yan Shilla, batagari guda 400 da suka buwayi mutane a cikin garin Yola da kewaye sannan har an kai su kotu domin yanke musu hukunci.

Ya kuma ce rundunar ta kama masu garkuwa da mutane mutum 121 sannan har ta ceto wasu daga cikin mutanen dake yankin masu garkuwa da mutane.

“A dalilin dokar kare hakin mata da yara kanana da gwamnati ta saka a jihar rundunar ta kama mutum 21 da suka ci zarafin mata da yara kanana sannan sun ceto wasu da aka yi wa fyade.

“Rundunar ta kuma kama wasu ‘yan fashi da makami da suka addabi mutane a hanyoyin Numan zuwa Gombe, Numan zuwa Jalingo da Ngurore zuwa Mayo Belwa.

Adamu ya ce manyan bindigogi kiran AK47 guda 20, bindigogi masu kiran G3, bindigan kirar single barrel guda 7 na daga cikin makaman da suka kwato daga hannun bata garin da suka kama.

Ya ce sauran makaman da suka kwato sun hada da bindigogi kirar hannu guda 11, harsasai 600, motoci 8 da dai sauran su.