Uwargidan gwamnan Bauchi ta raba wa kungiyoyin mata manoma tallafin taki kyauta

A ranar Litinin ne uwargidan gwamnan jihar Bauchi Aisha Mohammed ta raba wa kungiyoyin mata manoma takin zamani kyauta domin inganta noman ranin da ake gab da farawa a jihar.

Akalla kungiyoyin mata 20 ne suka amfana da tallafin Aisha.

Aisha ta ce ta raba takin ne domin mara wa gwamnati baya wajen samar da isasshen abinci a jihar.

Ta yi kira ga mata da su saka hannun jari a ayyukan noma domin inganta tattalin arziki a jihar.

Bayan haka Aisha ta yi bayanin cewa ta tsara shiri domin horas da mata yadda ake monan ridi a jihar.

“Tallafin da muke badawa mun fi tallafa wa kungiyoyin mata ne sannan nan ba da dadewa ba za a horas da mata yadda ake noman ridi.

Da take tofa albarkacin bakinsa wakiliyar kungiyar ‘mata manoma a jihar’ Hajiya Habiba Ajiya ta mika godiyar ta ga uwargidan gwamnan jihar Aisha Mohammed

Habiba ta ce raba takin zamani kyauta ga mata da uwargidan gwamnan ta yi hanya ce da zai taimaka wajen inganta aiyukkan noma a jihar.