Kullum maigida na sai ya jibge ni, wai na cika narkan Tuwo – Inji Fiddausi matar Haruna a Kaduna

A kotun Shari’a dake Magajin Gari jihar Kaduna wata matar aure Firdausi Sulaiman ta kai karan mijinta Aruwa Haruna tana nrokon kotu ta raba auren su na shekara bakwai saboda jibga da take sha wurin sa.

Sannan kuma ta roki kotun ta ba ta damar ta ci gaba da rike ‘yar su daya da suka haifa.

Ta bayyana a kotu cewa ta gaji da auren Haruna saboda jibgar ta da ya ke yi sannan da bada dalilin haka wai ta cika cin abinci a gidan.

Firdausi ta ce saboda tsananin rashin yarda maigidanta Haruna kulle kitchen din su ya ke yi duk dare da kwado.

” Da ma ni auren dole aka yi min da Haruna tun ina shekaru 16.

“Tun da na auri Haruna ban taba yin shekara daya a dakin mijina batare da ya kora ni gidan iyaye na ba.

“Haruna ya hana kawaye na zuwa gidanmu sannan ya hana ni zuwa gidajen su.

Ta ce da ta gaji sai ta bayyana wa iyayen ta halin da take ciki inda su iyayen suka fadawa mahaifiyar Haruna wacce ta shaida musu cewa Haruna na fama da iskokai ne.

Lauyan dake kare Haruna, M. K Mustapha ya tabbatar cewa Haruna baya fama da iskokai kamar yadda Firdausi ta fada a kotun.

“Haruna baiyi kama da mai fama da iskokai ba domin shi injiniya ne dake aiki da gwamnatin jihar Katsina.

Bayan ya saurari bangarorin biyu alkalin kotun Nuhu Falalu ya dage shari’a zuwa ranar 4 ga Oktoba.

Ya kuma umurci lauyan Haruna da ya kawo iyayen Haruna domin sassanta ma’auratan a zaman da kotun za ta yi na gaba.