‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindigan biyu a jihar Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ta kashe wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane guda biyu a Ajaokuta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ayuba Ede ya ce ‘yan sanda sun kashe ‘yan bindigan biyu a daidai suna fashi a ahanyar Ajaokuta a daren Talata.

Yan sanda sun yi musu diran bazata, suka surfafe su da ruwan harsahi har Allah ya basu sa’an kwantar da biyu daga cikin su, uku kuma suka arce amma fa da munanan rauni a jikin su.

Ede ya ce maharan su biyar ne suka tare hanyar, biyu sun mutu sannan uku sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.

Ya ce rundunar ta fara farautan sauran maharan da suka gudu.

Ede ya ce an kwato bindiga kirar AK47 da na katako guda biyu, manyan wayar salula guda 25, katin ATM na bankin FirstBank dake dauke da sunan Mohammed Jamiu da kudi duk a cikin kayan da ‘yan sanda suka kwato a hannun maharan.

Gwamnan jihar Yahaya Bello ya jinjina namijin kokarin da ‘yan sandan suka yi.

Aiyukkan mahara ya zama ruwan dare a Najeriya domin a cikin wannan mako PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa mahara sun kashe mutum sama da 200 a fadin kasar nan a makon da ya gabata.

Rahoton ya kuma nuna cewa a cikin makon da ya gabata an sace akalla mutum 137 a kasar nan.

An samu adadin ne daga rahotannin jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai ke wallafawa da kuma jin ta bakin iyalan mamata da na waɗanda aka yi garkuwa da su.