Kungiyar ma’aikatan Kotuna ta janye yajin aikin da ta shafe kwanaki 64 ta na yi

Kungiyan ma’aikatan kotunan kasar nan JUSUN ta janye yajin aikin da ma’aikatan ta suka shafe kwanaki 64 suna yi a Najeriya.

Sanarwar janye yajin aikin na kunshe a wata takarda wanda kungiyar ta fidda ranar Laraba bayan doguwar ganawa da ta yi da babban jojin Najeriya Mohammed Tanko, ministan kwadago Chris Ngige da kungiyar Alkalai NJC suka yi.

JUSUN ta janye yajin aikin ne duk da gwamnati ba ta biya musu bukatun su ba, sai dai ta ce bakin da babban Jojin Najeriya ya sa da kuma kungiyar Lauyoyi na Kasa ya sa suka janye yajin aiki.

Babban dalilin da yasa ma’aikatan kotunan kasar nan ke yajin aiki sun hada da neman gwamnatocin jihohi su amince kotuna su ci gashin kansu kamar yadda dokar kasa ta gindaya.

Gwamnoni sun ki amincewa da haka duk da ko shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar iko na tabbatar wa bangaren shari’a cin gashin kanta.

kungiyar ta ce kada a muzguna wa wani ma’aikaci a dalilin yajin aikin da kungiyar ta yi sannan kuma duk wasu hakkoki na ma’aikata da ya kamata a basu a tabbata an biya su.

A karshe kungiyar ta ce ba wai shikenan ba, za aci gaba da tattaunawa har sai hakan su ya cimma ruwa.

Kafin wannan sanarwa, gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan ma’aikatan kotuna da na Majalisun Dokokin Jihohi su gaggauta yanke yajin aikin da su ke yi tsawon watanni biyu, su koma bakin aikin su.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Ngige ya yi masu gargadin cewa idan ba su koma aiki ba, to Gwamnatin Tarayya za ta tilasta wa kan ta yin amfani da dokar rike albashin wanda bai je aiki ba, a hana shi tsawon watannin da ya yi fashi bai je aikin ba.

Wannan gargadi dai na nufin gwamnati ta kasa shawo kan lamarin, abin da kawai ya rage shi ne a yi baram-baram tsakanin ta da kungiyoyin JUSUN da ta Ma’aikatan Majalisun Jihohi.

Ngige ya nuna matukar damuwa ganin yadda kotunan kasar nan da Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya kakaf ke kulle ba su aiki tsawon watanni biyu, ba tare da wani dalilin kulle su ba.”

“Gwamnatin Tarayya ta damu ganin yadda bangarorin JUSUN/PASAN da Kungiyar Gwamnoni su ka kasa cika alkawurran da su ka cimma a yarjejeniyar baya-bayan nan da aka kulla a gaban Kwamitin Shugaban Kasa, wadda a wurin taron har Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa (NLC) ya halarta.”

Daga nan ya roki su gaggauta komawa aiki, domin rufe kotunan Najeriya ya damalmala matsalar shari’u da wasu bangarorin ayyukan da su ka jibinci tsaro ko kula da masu aikata manya da kananan laifuka.