‘Yan bindiga sun sace sama da mutum 20 a unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha, Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 20 a unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha, karamar hukumar Chikun.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Mohammed Jalige wanda ya sanar da haka ranar Juma’a wa tashar ‘ChannelsTv’ ya ce ‘yan bindigan sun far wa unguwar Gimbiya da misalin karfe daya na dare a lokacin da mutane ke kwance suna barci.
Jalige ya ce ‘yan bindigan sun shiga unguwar dauke da manyan makamai suka yi ‘kan mai Uwa da wabi’ da a dalilin haka mutum biyu suka mutu.
Ya ce rundunar ta fantsama farautar maharan domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
PREMIUM TIMES ta nemi samun karin bayani daga Jalige amma abin ya ti cura don bai amsa sakon da aka aika masa ba.
Wani mazaunin unguwan, Gyara Guga ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan hari sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin yawan mutanen da maharan suka sace ba.
Idan ba a ranar 31 ga watan Oktoba 2021 ‘yan bindiga sun sace mutum 70 a cocin Emmanuel Baptist dake kauyen Kakau Daji.
Sannan a kauyen Unguwar Ayaba mazauna kauyen na ta yin hijira zuwa kauyen Unguwar Gimbiya domin guje wa maharan da suka addabe su.
A jihar Kaduna karamar hukumar Chikun na daga cikin kananan hukumomin da ‘yan bindiga suka addaba.