Kotu ta bada belin barawon babur kan Naira 100,000

A ranar Juma’a ne kotun majistare dake Ogudu ta bada belin wani barawon babur Lukemon Odewole mai shekara 33 kan Naira 100,000 bayan an kama shi da laifin sata.

Odewole ya saci babur din kamfanin Domino Pizza’s wanda suke dawainiyar kai abincin da aka yi Oda.

Dan sandan da ya shigar da karan Sunday Bassey ya ce Odewole ya saci babur din ne ranar 17 ga Nuwanba da misalin karfe 5:32 na yamma a
Layin Ramat Kolawole a Ogudu GRA.

Bassey ya ce masu gadin wurin ne suka kama Odewole yayin da yake kokarin guduwa da babur din Wanda suka damkashi hannun ‘yan sanda.

A lissafe dai kudin baburi din ya kai Naira 550,000 sannan yada da lambar rajista GGE 269 QD.

Alkalin kotun ta bada belin Odewole sannan ta ce zai gabatar da shaidu biyu dake aiki kuma suke biyan gwamnatin jihar Legas haraji na tsawon shekara biyu.