ZAMFARA TA DAGULE: Mutanen Zamfara sun shiga halin-ni-‘ya-su, yayin da mahara su ka datse hanyoyi

Al’ummar Ƙaramar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara sun koka ga gwamnati, saboda datse masu hanyoyi da ‘yan bindiga ke yi.

A ranar Talata ce ‘yan bindiga su ka datse tituna biyu da ake shiga ko fita zuwa Shinkafi.

Hanyoyin guda biyu sun haɗa da titin Shinkafi-Ƙaura Namoda-Gudau da kuma Shinkafi-Isa-Sabon Birni.

“An shafe kwanaki da yawa su na tare motoci, kamar a ranar Alhamis sun tare hanyar Shinkafi zuwa Kaura Namoda, su ka kama motoci 15, a ciki su ka ƙone guda ɗaya.” Haka Sardaunan Shinkafi, Aliyu Shinkafi ya shaida wa wakilin mu.

Sardaunan Shinkafi ya ce ‘yan bindiga masu biyayya ga gogarma Bello Turji sun sha alwashin cewa ba za su sake barin jama’a su je su ci kasuwar Shinkafi ba.

Kasuwar Shinkafi na ɗaya daga cikin manyan kasuwannin Arewa maso Yamma masu ci kowane mako.

Wani ɗan cikin Shinkafi da ya nufi gida daga Gusau, ya shaida wa wakilin mu cewa datse hanyar ya ritsa da shi.

“Allah dai ya sa ina da sauran shan ruwa a gaba kawai. Amma lamarin ya yi muni. Sun tare mu a cikin daji. Su ka hana mai fitowa daga Gusau ya koma Gusau ko ya yi gaba zuwa Shinkafi.

“Su ma waɗanda su ka fito daga Shinkafi, aka hana su komawa cikin gari, kuma aka datse masu hanyar wucewa zuwa Gusau. Haka su ka jera kwanaki uku su na datse hanyoyin, daga Talata, Laraba da Alhamis.” Inji Mohammed Humility.

Shi ma Adam Barau, wanda direba ne, ya cewa wakilin mu tilas ya fasa tafiyar da ya yi niyyar yi, “saboda ‘yan bindiga sun hana zuwa Gusau, sun tare Mahaɗar Badarawa zuwa Birnin Yero, kuma sun hana bi ta Moriki zuwa Mahaɗar Boko.

“Da ido na sai da na ƙirga motoci biyar duk ‘yan bindiga sun banka masu wuta su na ci bal bal bal. Na ga mutane a kwance shame-shame.

“Akwai wani Injiniya Silame, wanda ma’aikacin gwamnati ne, shi motar sa su ka buɗe wa wuta. Su ka yi mata raga-raga da ruwan harsasai. Allah ne ya sa Silame na da sauran kwana a gaba kawai.

Humility ya ce ya ga motoci aƙalla 20 cikin daji duk mutanen da ke ciki sun tsere, a tsakanin Shinkafi zuwa Kaura Namoda. A hanyar Shinkafi zuwa Isa kuwa, an kashe mutum uku.

Wani lauya mai suna Nasiru Shehu, har ya kai Kaura Namoda, amma aka ba shi shawara aka ce kawai ya hanzarta komawa baya, kada ya kuskura ya ƙara gaba.

“Ce min su ka yi jami’an tsaro na can na fafatawa da ‘yan bindiga. Na jira har sa’o’i biyu a Ƙaura Namoda. Da na ga abin ba mai ƙarewa ba ne, sai na haƙura, na dawo baya.” Inji shi.

Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara bai ɗauki wayar kiran wakilin mu ba, kuma bai maida masa amsar saƙon tes da ya yi masa ba.