‘Yan bindiga sun kashe mutum 41 a cikin mako daya a Najeriya

Akalla mutum 41 ne suka gamu da ajalinsu a hannun ‘yan bindiga a cikin makon da ya gabata a kasar nan.
Daga cikin yawan mutanen da aka kashe akwai jami’in tsaro na SSS mutum daya sannan sauran ‘yan garin hula.
An sami adadin yawan mutanen da aka kashe ne daga rahotannin da jaridun Najeriya suka buga a cikin makon.
Rahoton ya nuna cewa an samu raguwar kashi 50% a yawan mutanen da aka kashe daga mutum 123 a makon jiya zuwa mutum 41 a makon da ya gabata.
Sannan kuma an samu raguwa a yawan jami’an tsaron da ake kashewa daga hudu a wancan mako zuwa jami’i daya a makon da ya gabata.
Mafi yawan kisan da aka yi a wannan mako ya auku ne a Arewa maso Yammacin kasar nan sannan da daya a yankin Gabashin kasar.
Zamfara
A harin da aka kai garin Kurya Madaro dake karamar hukumar Kauran Namoda ‘yan bindiga sun kashe mutum 18 inda a ciki akwai maza, mata da yara kanana.
Wani mazaunin garin Mohammed Kurya ya bayyana wa manema labarai cewa maharan wanda a cikinsu akwai maza da mata sun shigo garinsu a kan rakuma da dawakai rike a hannuwan su bindigogi.
Katsina
A ranar Talata ‘yan bindiga sun far wa kauyen Yasore inda suka kashe mutum 10 sannan da dama sun jikkata.
Maharan sun kuma kona gidaje da shagunan mutane a kauyen.
Sokoto
‘Yan banga wanda aka fi sanin su da ‘Yan Sakai’ sun kashe mutum 11 a kauyen Mande dake karamar hukumar Gwadabawa.
Limamin kauyen na daga cikin wadanda aka kashe.
Mutanen da maharan suka harbe sun mutu nan take sannan wasu mutu hudu sun ji rauni.
Imo
Mahara sun kashe wani jami’in SSS mai suna Prince Nwachinaemere Ozuzu.
Maharan sun kashe Ozuzu yayin da yake hanyar zuwa wurin aiki a Owerri.