Yadda ‘Yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda suka kuma yi garkuwa da matar Alhaji Umaru

Mahara sun kai hari ofishin ‘yan sandan garin Nguroje, karamar hukumar Yola ta Kudu ranar Lahadi.

Bayan haka kuma a daidai suna kokarin afka wa ‘yan sanda wasun su kuma sun kai farmaki ne gidan wani attajiri a cikin garin inda suka yi garkuwa da matarsa dake jego.

Wannan abu dai ya auku ne ranar Lahadi da misalin karfe 2 na dare.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Sulaiman Nguroje ya sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Lahadi.

Nguroje ya ce ‘yan bindigan sun rabu gida biyu ne, bangare daya suka nausa ofishin ‘yan sanda bangare na biyu kuma suka shiga gari dibar mutane.

Wadanda suka nausa cikin gari sun fara dira gidan wani Alhaji Umar dake Nasarawo B, suka yi garkuwa da matarsa Hauwa umar wanda bata dade da haihuwa ba.

” Dabarar da suka yi shine su rabu gida biyu domin hana ‘yan sanda biyu su cikin gari daukar iyalan aljhaji Umaru.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Barde ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin ceto mai jegon da kuma kamo wadannan mahara.

A karshe ya yi kira ga mutanen gari da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri da min kamo bata gari a fadin jihar.