Shin, Ahmad Lawan ne dan majalisan da ya fi dadewa a majalisar dokokin Najeriya? Binciken DUBAWA

Ranar 25 ga watan Satumbar 2021, Chidi Odinkalu, farfesa, Lauya, marubuci kuma mai fafautukar kare hakkin dan adam ya yi ikirarin cewa sanata Ahmad Lawan ne dan majalisar dokokin Najeriya da ya fi dadewa a majalisar dokokin kasar fiye da dukkan sauran ‘yan majalisar da ke a yanzu.

Odinklau ya ce: “Abin da @DrAhmadLawan ba ya fada muku shi ne duk cikin ‘yan majalisar da ke @nassnigeria shi ne ya fi gogewa, domin tun 1999 bai taba rasa kujerar sa ba. #GoFigure,” farfesan kuma tsohon shugaban hukumar kare hakkin dan adam na Najeriya ya bayyana haka a shafinsa a yanar gizo.

Furucin Mr. Odinkalu martani ne ga wani mai amfani da shafin tiwita mai suna Dokun Ojomo (@DokunOjomo) wanda ya yi tsokaci kamar haka “Majalisar dattawa ba za ta iya hana Buhari karbar bashi ba. Sai dai a dorawa gwamnatocin baya laifin halin da muke ciki yanzu tun da su ne ba su yi tanadin gobe ba.” Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan

Wannan furuci da aka danganta da Lawan ya nuna goyon bayan sa kan basukan da shugaba Muhammadu Buhari ya karbowa a dadidai kuma shine kan gaba wajen dorawa gwamnatocin baya laifin matsalar tattalin arziki da Najeriyar ta fada cikin tsundum yanzu.

Basussukan da gwamnatin Buhari ta karbowa a kwanakin nan sun janyo kakkausar suka daga al’ummar Najeriya wadanda suka nuna fushinsu ga ‘yan majalisar da suka amince a karbi wadannan kudaden da yake ci wa mutanen Najeriya tuwo a kwarya.

‘Yan Najeriya na yi wa majalisar dokoki na kasar majalisar jeka na yi ka, ba su yi taka wa gwamnati birki kan abubuwan da suka ga bai dace a yi su ba. Sun zama bakin ganga kawai duk inda aka karkata aka buga za ta yi kara.

Sai dai kuma ba tun yanzu ba majalisar dokokin ta rika fitowa tana karyata hakan cewa ita fa tana yin abinda ya dace a koda yaushe kamar yadda yake a dokar kasa.

“Abin da na ke so in bai wa ‘yan Najeriya tabbaci akai shine , ba za mu goyi bayan a rika ciwo basussuka haka kawai don nishadi ba wanda ba amfanin jama’a za a yi da su ba”. In ji shugaban majalisar dattawa a watan Yunin 2021.

Ranar 14 ga watan Satumba shugaba Buhari ya bukaci amincewar majalisar dokokin ta amince masa ya ciwo wani karin bashi na dala billiyan 4.054 da euro milliyan 710, wanda zai hada da wani tallafin da ya nema na dala milliyan 125 a cikin shirin sa na ciyo bashi daga kasashen waje daga 2018 zuwa 2020.

Idan ba a manta ba, a watan Mayun 2021 shugaba Buhari ya sake neman amincewar majalisar domin karbar bashin dala billiyan 6.18 domin cike gibin kasafin kudin 2021 na naira trilliyan 5.6. Kasa da watanni biyu bayan haka a watan Yuli majalisar dattijai da sake samun wata bukatar bashin dala billiyan 6, da dala billiyan 8.3 da kuma euro milliyan 490. A cewar ofishin kula da basussuka na kasa (DMO) a karshen watan Satumba 2021 bashin Najeriya ya kai naira biliyan dubu 35.46.

Yadda wasu a gwamnatin shugaba Buhari ke zargin wai gwamnatocin baya ne ke da alhakin tsananin bashin da Najeriya ke fama da shi yanzu na harzuka jama’a sosai har da irin su Mr. Odinkalu wanda ya nuna cewa da yawa daga cikin wadanda ke gwamnatin Buhari sun kasasnce a gwamnatocin baya, har da shi kan shi Ahmad Lawan.

Da ya ke tsokaci dangane da wannan batu, wani mai suna Godwin A. ya dora laifi gwamnatocin baya ba shi wuyan yi kowa zai iya wage bakinsa ya ce ai a baya ne aka yi kaza da kaza, amma kuma ku da kuke akai yanzu me kuke yi dan ganin an gyara lamarin saboda masu zuwa a baya?

Wace irin rawa ka taka a majalisar a tsawon shekarun da ka yi wajen ganin an kaucewa matsalar da aka shiga yanzu?

Tantancewa

Domin tantance gaskiyar wannan furuci da Mr. Odinkalu yayi game da sanata Ahmad Lawan, Dubawa ta yi binciken tarihin dan majalisar da sauran ‘yan majalisan da suka fi dadewa a majalisun biuy- wato na wakilai da na dattawa.

Wane ne Sanata Ahmad Lawan?

An haife Ahmed lawan ranar 12 ga watan Janairu 1959, shi ne sanatan dake ke wakiltar yankin arewacin Yobe a inuwar jam’iyya mai mulki ta APC. An zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa na tara a watan Yunin 2019 bayan sami kuri’u 79 da ya kayar da abokin takararsa Ali Ndume wanda ya sami kuri’u 28 kacal.

Ahmed Lawan da shi aka bude majalisar tarayya a 1999 a matsayin sa na mai wakiltar Bade/Jakusko a majalirai wakilai ta tarayya. Ya sake cin zabe a 2003 ya kuma ci gaba da kasancewa a wannan mukami har zuwa shekarar 2007 lokacin da ya yi takarar neman kujerar sanata.

A shekarar 2015 sanata Bukola Saraki ya doke shi a zaben shugaban majalisar dattawa. Shekaru bayan nan sai ya zama shugaban masu rinjaye bayan da aka tsige sanata Ali Ndume a shekarar 2017. Ya cigaba da rike wannan mukamin har zuwa lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Duk da cewa sanata Ahmed Lawan ya kasance a majalisar tun 1999, Dubawa ta gano cewa ba shi ne kadai ke da wannan dogon tarihin da shi ka bude majalisar dokokin Najeriya a 1999 ba.

Hon. Nicholas Ebomo Mutu

Nicholas Mutu dan majalisa ne dake wakiltar Bomadi/Patani daga jihar Delta. Kamar Ahmed Lawan da shi aka bude kofofin majalisar tarayya a 1999 kuma har yanzu yana nan daram yana ci gaba da wakiltar mutanen sa. Shi dan asalin kabilar Ijaw ne kuma dan jam’iyyar PDP.

A yanzu haka ma shi ne shugaban kwamitin ma’adinan gas.

A Karshe

Sabanin zargin da Odinkalu yayi cewa Ahmed Lawan ne ya fi dadewa a majalisar dokokin Najeriya, akwai Mutu dake wakiltar jihar Delta a majalisar tarayya, shima kamar yadda aka bude kofofin majalisar da Lawan kuma yana nan daram a majalisar har yanzu haka shima Mutu, tun 1999 yana wakiltar mtanen sa.