YAJIN AIKIN LIKITOCI: Likitoci sun yi fatali da tayin karin kashi 25 bisa 100 na albashi, sun raina naira 25,000 matsayin alawus-alawus

Kungiyar Likitocin Cikin Gida ta NARD, ta yi fatali da tayin karin kashi 25 bisa 100 na albashi, kuma sun shure tayin naira 25,000 a matsayin kudaden alawuus-alawus, wanda za a yi wa likitocin tiyata da na bangaren aikin hakora.

A ranar Laraba ce dai Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince da wannan kari, lokaci kadan bayan likitocin sun fara yajin aiki.

Gwamnati ta mika wannan karin tayi ta cikin wata wasika a ranar 26 Ga Yuli, wadda Shugaban Hukumar Daidaita Albashi ta Kasa, wato NSIWS, Ekpo Nta ya sanya wa hannu.

Ku Rike Karin Ku, Ba Ma So – Likitoci:

Sai dai kuma Shugaban Kungiyar Likitocin Cikin Gida na Kasa, Emeka Orji, ya aiko wa PREMIUM TIMES da wata wasikar da ya aiko wa jaridar cewa su na sanar da Gwamnatin Tarayya cewa ba su son karin da aka yi masu din.

Haka kuma ya ci gaba da cewa dan karin alawus cikin cokalin da aka yi masu, shi ma ba su so.

Daga nan ya ce su kawai abin da su ke bukata shi ne Gwamantin Tarayya ta cika masu alkawarin da ta daukar masu a rubuce a cikin yarjejeniyar da su ka rattaba.

Ya ce duk wani abin da za a yi masu ba su bukata, sai fa a cika masu alkawarin karin albashi bisa tsarin COMESS da aka yi masu tun cikin 2009, amma aka kasa cikawa.

Wannan yajin aiki dai ya jefa harkokin kiwon lafiya a asibitocin kasar nan ciki rudani.