ASARI DOKUBO YA TADA TUBA: Ya ce zai iya murƙushe Gwamnan Ribas

Tsohon ɗan tawayen Yankin Neja Delta, Asari Dokibo, ya yi barazanar ragargaje Gwamnan Jihar Ribas, Siminalaye Fubara.
Cewa ya yi “idan Gwamna Fugara na neman bala’i, to ya gamu da bala’o’i”
A cikin shafin sa na Tiwita ya yi wannan barazanar a ranar Talata.
Asari bai ambaci suna ba, amma dai ya yi barazanar ce Ga Gwamnan Jihar Ribas, tare da wasu da AK 47 zagaye da shi.
“A Dokar Najeriya shi da kuma ni ɗaya muke.”
“Fitina barci ce, mai neman tashe-tashen hankula zai tayar da ita.”
Da alama Asari hasala ya yi da Gwamna a wani labarin da aka ce Gwamnan ya ragargaji Asari, saboda fito da bindigogin da ya ke yi
Asari ya ce da ya ga dama da ya hargitsa Ribas lokacin zaben Gwamna, saboda maguɗi aka yi
Asari ya ce ba ya so a yi asarar rayuka shi ya sa ba a yi rigima ba a zaɓe
Ya ce idan ya tada fitina, “To Boko Haram za’a ga wasa ne”