YAJIN AIKI: Nan ba da dadewa ba za mu sake zama da kungiyar likitoci NARD – Inji Abbas

Kakakin majalisar wakilai na kasa Tajuddeen Abbas a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokari domin ganin ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar likitoci NARD suka fara.

Abbas ya fadi haka ne wa manema labarai a fadar shugaban kasai bayan kammala ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu.

Kungiyar likitoci NARD ta fara yajin aiki ranar Laraba.

Biyan alawus din sadaukar da rai yayin aiki, biyan kudin horas da ma’aikata, daukan isassun ma’aikata, biyan basussukan albashin ma’aikata duk na daga cikin bukatun kungiyar.

“Mun nada kwamitin da Shugaban masu rinjaye na majalisar zai shugabanta domin ganin mun biya bukatun kungiyar.

“Ina tabbatar da cewa idan har muka samu nasaran biyan daya ko biyu daga cikin bukatun likitocin za su dawo aiki.

Abbas ya ce shugaba Tinubu ya roki alfaramar kungiyar da su kara hakuri musamman yadda har yanzu ba shi da cikakken bayanai kan matsalolin da suke fama da su.

“Shugaba Tinubu ya ce a aika da duk bukatun kungiyar ga shugaban ma’aikatan fada domin ya samu yin nazari a kansu. Ina sa ran cewa Nan ba da dadewa ba gwamnati za ta dauki kwakwaran matakan kawar da matsalolin da suke fama da su.

Kungiyar likitoci NARD, ta fara yajin aikin ‘Sai baba ta gani ‘ ranar Laraba

Shugaban kungiyar Emeka Orji ya sanar da haka a daren Talata.

Wannan sanarwar ya zo ne bayan zaman da kungiyar ta yi da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abass.

Abbas ya yi bayanin cewa zai kara ganawa da kungiyar ranar Alhamis.