RASHIN TSARO: ‘Yan bindiga sun kashe kauyawa 7 a jihar Bauchi

Akalla mutum bakwai ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Kaja dake karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi ranar Talata.
Mazauna kauyen Kaja sun ce maharan sun dira kauyen da karfe 10 na dare suna ta barin wuta da bindigogin su.
Sun ce a ranar Laraba da safe ne suka yi jana’izan mutanen da maharan suka kashe.
Wani da harin ya faru a idon sa ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa kungiyar ‘yan banga sun yi batakashi da maharan sai dai kuma maharan sun kashe daya daga cikinsu.
Ramuyar Gayya
Mazauna kauyen Kaja sun ce akwai yiwuwar harin da maharan suka yi ranar Talata ramuwar gayyan harin da aka kai wa maharan a maboyar su ranar Litini.
A wannan hari jami’an tsaro sun kashe mutum biyu daga cikin maharan.
Wani manomi Ibrahim Ayuba ya ce bana rashin tsaro ya tabarbare a kauyen inda hakan ya sa ba zai iya yin noma ba.
Sabon kwamishinan tsaro na jihar Auwal Muhammad ya ce rundunar ta sa himma domin kawar da rashin tsaro a jihar.
Muhammad ya ce sun ceto mutum 10 a maboyar maharan dake dajin Lame-Burra ranar Litini.