‘DIPHTHERIA’: Mutum biyu sun mutu a jihar Bauchi

Hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin lafiya na matakin farko ta jihar Bauchi BSPHCDA ta bayyana cewa cutar Diphtheria ta barke a kananan hukumomi shida a jihar.

Shugaban hukumar Rilwanu Mohammed ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai ranar Laraba a garin Bauchi.

Mohammed ya ce daga Janairu 2023 zuwa yanzu hukumar ta yi wa mutum 58 gwajin cutar daga cikin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar.

Ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa mutum uku sun kamu sannan biyu daga cikin su sun mutu a karamar hukumar Jama’are.

“ Mafi yawan mutanen da suka fi kamuwa da cutar makiyaya ne da yara kanana da basu allurar rigakafin cutar ba.

“Yara ‘yan wata takwas zuwa shekara hudu sun fi kamuwa da cutar sannan mun samu yaro dan shekara 7 da ya kamu da cutar.

Mohammed ya ce gwamnati ta sa a rufe duk makarantun dake karamar hukumar Jama’are musamman yadda aka samu wani dalibi da cutar.

“Za Kuma mu zage damtse wajen ganin mun yi wa duk yara allurar rigakafin cutar musamman a makarantar da cutar ta bullo.

Ga abubuwa 9 game da cutar Diphtheria

1. Menene cutar Diphtheria

Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa wa.

Babu babba ko yaro a yadda Cutar ke yaduwa amma jami’an lafiya sun ce cutar ya fi kama yara kananan musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.

2. Hanyoyin kamuwa da cutar.

Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar sumba musamman idan ana yin sumban da mutane daban-daban.

Cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.

Idan mai dauke da cutar ya yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.

Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu fama da cutar suka yi amfani da su kamar chokali, Kofi, hakichin da sauran su.

3. Mutanen da suka fi kamuwa da cutar

Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.

4. Alamun cutar

Akan gane alamun cutar bayan ranar farko zuwa rana ta 10 bayan kamuwa da cutar.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaron, idanun za su Yi jajawur, tari da Kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa da a kusa da makogwaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi da hadiyan abinci.

5. Abin da ke haddasa cutar

Kwayoyin cutar ‘Corynebacterium diphtheria’ ne ke haddasa cutar inda yakan kama hanci, makogwaron da fatara mutum.

Rashin tsaftace muhalli na haddasa cutar.

6. Ire-iren cutar Diphtheria

Cutar diphtheria ya rabu biyu inda akwai ‘Classic respiratory’ wanda kan kama hanci makogwaro sannan da ‘Cutaneous’ wanda kan kama fatar mutum.

7. Hanyoyin gane cutar a jikin mutum

Jami’an asibiti na iya gano cutar daga alamun kamuwa da cutar da suka fara nunawa a jikin mutum kokuma idan aka Yi wa mutum gwajin cutar.

8. Maganin cutar

Wanda ya kamu da cutar zai killace kansa sannan maganin ‘Antibiotices’ na kawar da cutar daga jikin mutum.

Sannan ruwan dumi akai-akai na taimakawa wajen rage zafi da Kumburin makogwaro.

Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar

A. Yin allurar rigakafi.

B. Saka takunkumin fuska musamman idan za a shiga cikin mutane.

C. Kare baki da hanci idan za a yi tari ko atishwa.

D. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

E. Zuwa asibiti da zaran an kamu da zazzabi ko idan ba a gane lafiyar jiki ba

Bullowar Cutar Shawara.

Bayan haka hukumar ta ce cutar shawara ta kara barkewa a jihar.

An gano haka ne bayan sn samu rahotan cewa ana zargin mutum 248 sun kamu da cutar a kananan hukumomin Dambam, Ganjuwa da Jama’are.

Hukumar ta ce an samu tabbacin mutum biyar sun kamu da cutar.

Rashin gaggawan samun sakamakon gwajin na daga cikin matsalolin da hukumar ke fama da su a jihar.