Yadda gobara ta babbake ofishin babban editan PREMIUM TIMES ta kai farmaki dakin tattara labarai a Abuja

” Muna zaune a cikin ofishin mu sai muka rika jin rukugin wuta hayaki na fitowa ta ofishin babban editan Premium Times, Mojeed Musikilu. Dukkan mu ka dunguma zuwa ofis din sa domin mu tabbatar daga nan ne utar ta shi. Isar mu ke da wuya sai muka ga ashe ya fita zuwa masallaci kuma kofar a kulle take.
” Haka mu ka yi da karfin tsiya muka balla ofis din, amma shiga ya gagara saboda tirnikewar hahayi da wuta.” Wadannan suna kalaman mataimakin babban Editan Kamfanin, Bisi Abidoye a lokacin da yake bayanin abinda ya auku bayan an kashe wutan.
Wasu daga cikin ma’aikatan da ke cikin ginin suka kawo dauki. Sun rika amfani da na’urar kashe wuta da aka ajiye a kusurwowin ginin kafin isowar yan kwana-kwana masu kashe gobara.
Ba a iya fidda ko tsinke daga ofishin babban editan kamfanin ba inda daga nan ne gobarar ta taso.
” Babu abin da aka iya fiddawa daga ofishin sa, baya ga takardu da na’urorin aiki duk sun babbake.