Sojojin Najeriya sun sheƙa ‘yan bindiga 250 lahira, sun damƙe 600, sun kuɓutar da dubban mutane daga hannun su -Irabor

Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Lucky Irabor, ya ce daga lokacin da aka kulle wayoyin sadarwa a wasu sassa, an bindige ‘yan bindiga 250 kuma an damƙe 600 a yankunan jihohin Zamfara, Sokoto, Neja da Kaduna.
Irabor ya yi wannan ƙarin haske a lokacin da ya ke wa manema labari bayani, a ranar Alhamis, wurin taron mako-mako da Jami’an Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa ke shiryawa, bisa jagorancin Femi Adesina.
Babban Hafsan Tsaron Ƙasa Irabor ya ce an kuɓutar da dubban waɗanda aka yi garkuwa da su cikin makonni biyar a jihohin Kaduna, Neja, Sokoto, Katsina da Zamfara.
Ya ce babban burin gwamnati shi ne a ga an samu wanzuwar zaman lafiya a cikin al’umma, ta yadda za su riƙa samun kayayyaki na more rayuwar da inganta rayuwar al’ummar su.
“Mu kuma sojoji aikin mu ne mu ga mun kare rayuka da tabbatar da wannan zaman lafiya.
“A rahotonnin da na ke samu zuwa ranar Litinin ɗin nan, an kashe ‘yan bindiga 250, an kama wasu 600, kuma za a ci gaba, ba za a saurara masu ba. Sannan kuma adadin waɗanda aka kashe da kamawa din zai iya ƙaruwa daga ranar Litinin zuwa yau Alhamis.
“Ina kuma sanar da cewa an ceto wasu da yawa, waɗanda mahara su ka kama su ka tilasta su ɗaukar bindiga, a dazukan Zamfara, Sokoto da Katsina.”
Shugaban ISWAP, Al-Barnawy Ya Mutu -Irabor:
Da aka tambaye shi batun haƙiƙanin labarin da ake bazawa na mutuwar shugaban Boko Haram ɓangaren ISWAP, Abu Mus’ab Al-Barnawy, sai Irabor ya ce tabbas ya mutu.
“Ina tabbatar maku cewa Abu Mus’ab ya mutu. Tuni Abu Mus’ab ya zama gawa.”
Duk da ci gaba da kisa da kama ‘yan bindiga da ake yi, Irabor ya ce har yau akwai su cikin dazuka da dama a Arewa maso Yamma.
“Amma wasun su ƙalilan su na dannawa cikin yankin Arewa ta Tsakiya, su ma ɗin mu na ɗaukar mataki a kan su ta yadda ba za su warwatsu zuwa inda ba za a iya kakkaɓe su ba.
Irabor ya ce zuwa yanzu dai dama ‘yan ta’adda 1,800 sun yi saranda.