Yadda aka sa tsinin biro aka caccake idanun naira biliyan 15 a Hukumar NEPZA cikin shekara biyu

Yayin da Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da bankaɗo yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya ke karkatar da kuɗaɗe, cikin wannan makon kuma an bankaɗo yadda aka karkatar da naira biliyan 15 a Hukumar Kula Sa-ido kan Kayan da ake Fitarwa daga Najeriya, wato ‘Nigeria Export Processing Zones Authority’ (NEPZA).

Ofishin Mai Binciken Kuɗi na Tarayya, wato Auditor General of the Federation, ya bankaɗo yadda Ma’aikatar Bunƙasa Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta kafa wani kamfani a ƙarƙashin NEPZA, ba tare da amincewar Shugaba Muhammadu Buhari ba, aka yi amfani da kamfanin aka karkatar da naira biliyan 15, daga 2017 zuwa 2019.

Kamfanin mai suna NZESCO, an kashe naira miliyan 1.3 aka yi masa rajista ta hanyar bijire wa dokar Najeriya, wadda ta ce kafin Ma’aikatar Bunƙasa Masana’antu da Kasuwanci ta kafa kamfanin, tilas sai da sa hannu da amincewar shugaban ƙasa.

Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ya gano cewa ba a lokaci ɗaya aka karkatar da kuɗaɗen ba, an riƙa kamfata ne jifa-jifa, ana narkawa cikin asusun kamfanin NZESCO, wanda shugaban ƙasa bai san an kafa shi ba.

Wannan karafkiya dai ta faru a lokacin da Okechukwu Enelemah ne Minista a ma’aikatar, wato a shekarun 2017 da 2019.

A bayanin da Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ya yi, ya ce bayan masu bincike sun gano cewa an karkatar da naira biliyan 15 ba bisa ƙa’ida ba, sun nemi a ba su sunayen daraktocin kamfanin NZESCO amma Ma’aikatar Bunƙasa Masana’antu da Kasuwanci ta hana su.

Sun kuma nemi sanin adireshin kamfanin NZESCO, shi ma ba a ba su ba. Haka nan kuma sun nemi ganin lambar rajistar kamfanin, ita ma ta gagara.

Daga nan Ofishin Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya ya umarci ma’aikatar ta yi wa Majalisa bayanin yadda aka yi da kuɗaɗen, kuma ta bayar da jadawalin ayyukan NZESCO da dukkan yadda aka zuba kuɗaɗe a asusun kamfanin. Ofishin bincike ya ce idan ba a yi haka ba kuwa, to za a hukunta masu hannu a lamarin.

Shuka A Idon Makwarwa:

Makonni biyu da suka gabata, wannan jarida ta buga labarin yadda Ma’aikatar Gona ta kasa yin bayanin yadda ta yi da naira biliyan 48 cikin 2019.

Ma’aikatar Harkokin Gona ta daɗe ta na dawurwurar kasa yin gamsasshen bayanin yadda ta kashe zunzurutun naira biliyan 48, a cikin 2019, maƙudan kuɗaɗen da aka kashe ba a cikin kasafin kuɗin shekarar ba.

Wani bincike da Ofishin Binciken Kuɗaɗe na Gwamnatin Tarayya ne ya gano haka kwanan nan.

Rahoton ya ce Ma’aikatar Harkokin Noma da Bunƙasa Karkara ta yi sakaci wajen yin abin da bai dace ba da kuɗaɗen, a gafe ɗaya kuma ta riƙa samun cikas wajen zuba kuɗaɗe ta yi ayyukan da ke cikin tsarin kasafin kuɗin shekarar.

Rahoton ya ce Ma’aikatar Noma ta samu cikas ɗin ne saboda ba ta ɗauki matakan da su ka dace ba, wajen biyan ‘yan kwangilar da su ka cancanta haƙƙin kuɗaɗen su ba.

Masu bincike sun yi amfani da Saɗara ta 2906 (II) ta Dokar Ƙa’idojin Kuɗaɗe wadda ta ce, “dukkan wata kwangila tilas ta kasance ta na cikin kasafin kuɗaɗe tare da tabbatar da cewa akwai kuɗaɗen da aka ware mata a cikin kasafin. Wato dai ana nufin ba za a amince da biyan duk wata kwangilar da kuɗaɗen yin ta ba ya cikin kasafin kuɗi ba.”

Rahoton wanda Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya da kan sa ya fitar, ya ce Ma’aikatar Gona ta yi amfani da fiye da Naira biliyan 7 daga cikin kasafin 2019, ta biya wasu ayyukan da aka yi cikin 2018, wanda wannan babban kuskure ne.

“Don me za a zabge Naira biliyan 7 daga cikin kasafin 2019 a biya aikin da aka yi cikin 2018, alhali an ware kuɗin aikin tun da farko a cikin 2018 ɗin?” Inji rahoton binciken.

A cikin wata wasiƙar da Ma’aikatar Harkokin Noma ta aika a ranar 3 Ga Nuwamba, 2020 ta bada haƙurin abin da ta aikata, kuma ta ce Hukumomin Yaƙi da Cin Rashawa na nan na binciken badaƙalar.

Duk da alƙawurran da Shuagaba Mauhamamdu Buhari ya yi na bunƙasa harkokin noma, har yau ma’aikatar noma ba ta samun kuɗaɗen da su ka kamata. Waɗanda ta ke samun kuma, ana ɗibar da yawa daga cikin su a karkatar ko a waske da su.

Saboda rashin iya aiki ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami tsohon Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono, a cikin Satumba, 2021.