RASHIN JITUWA: ‘Yan sanda sun damke Zubairu da ya sheme matarsa ta fadi matacciya a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani magidanci Yusuf Zubairu mai shekara 26 da laifin kashe matarsa Fatima Hardo mai shekara 23 da ya rika dukar matar sa saboda sabani da ya kaure a tsakanin su har sai da aika ta lahira.

Kakakin rundunar Lawan Adam ya ce Zubairu ya kashe Fatima ranar 27 ga Disamba da misalin karfe 11:30 na safe a gidan su dake kauyen Baldi a karamar hukumar Sule-Tankarkar.

Adam ya ce a wannan ranan rashin jituwa ya shiga tsakanin Zubairu da matar sa Fatima cikin fushi Zubairu ya suntumi dauki reshen ice ya sheme Fatima da shi. Nan take ta yanke jiki ta fadi.

Adam ya ce rundunar ta samu labarin aika-aikan da Zubairu ya aikata bayan wani Bulama Muntari-Ubale mai shekara 65 wanda aka fi sani da Sallau ya kawo kara a ofishinsu.

Ya ce nan da nan jami’an tsaro suka ba zama zuwa gidan Zubairu inda suka iske Zubairu ya ji wa wata makwabciyar su mai suna Rabi Lawan rauni da ta zo rabon fada sannan kuma can gefe matarsa tana kwance a ƙasa.

Adam ya ce zuwa yanzu Zubairu na tsare a ofishinsu sannan Rabi likitoci na duba ta amma Fatima ta rasu.

Ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano abin da ya faru a gidan Zubairu.