ƘUDIRIN GYARAN ZAƁE DA MAJALISAR DATTAWA: Hanyar jirgi daban, ta mota daban -Sanata Adamu

Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa babu ruwan sanatoci da dokar gyaran zaɓe, bai kamata su tsoma hannun su a sha’anin zaɓen fidda-gwani ba.

Adamu wanda ke wakiltar yankin Jihar Nassarawa ta Yamma, ya shaida wa manema labarai a Lafiya cewa ya yi farin ciki da Shugaba Muhammadu Buhari bai sa wa dokar hannu ba.

Adamu ya ce bai ga dalilin da zai sa Majalisar Dattawa ta shiga lamarin da ya shafi tsarin zaɓen fidda-gwanin jam’iyyun siyasa ba.

“Kowace jam’iyya ta na da dokokin ta da tsarin ta. Don me za a ce sai an ce ga yadda jam’iyya za ta yi zaɓen fitar da gwanin ta.

“Na yi murna da farin ciki ganin Shugaba Buhari ya yi zurfin tunani da hangen nesa, har ya ƙi sanya wa ƙudirin hannu domin ya zama doka.

“Ina mamakin yadda za a zaɓi mutum ya zama sanata a ƙarƙashin wani tsari. Amma bayan ya hau ya yi ƙememe ya ce sai an canja tsarin.” Inji Adamu, wanda tsohon gwamna ne a jihar Nasarawa, kuma ɗan jam’iyyar APC ne.

Ya ce idan majalisa ta koma zama a cikin Janairu, za a zauna a san abin yi a kan batun sauran baturuwan da ke cikin ƙudirin.

Cikin makon jiya ne Kakakin Shugaba Buhari ya ce tantagaryar rashin mutunci ne idan ‘yan majalisa na APC suka nemi tirsasa dokar da Buhari ya ƙi sa wa hannu.

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa zai yi wahalar gaske a ce mambobin Majalisar Tarayya da na Dattawa daga ɓangaren APC su goyi bayan tirsasa kafa dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi sa wa hannu, saboda tilas su yi biyayya ga jam’iyyar su.

Kakakin Yaɗa Labarai na Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka a ciki wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels ya yi da shi.

Adesina ya ce duk tantagaryar rashin mutuncin ‘yan majalisa na ɓangaren APC, ba su yi gangancin bijire wa Shugaba Buhari ba.

Jam’iyyar APC ce dai ke da mafi rinjayen mambobin Majalisar Tarayya da mafi rinjayen Sanatoci.

Ciki makon jiya ne Buhari ya sa ƙafa ya yi fatali da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2021, bayan da majalisa ta aika masa tun a ranar 29 Ga Nuwamba, domin ya sa hannu.

Sai dai kuma an haƙƙaƙe cewa gwamnonin Najeriya ne su ka ja ra’ayin sa har ya ƙi sanya wa dokar hannu, saboda batun zaɓen fidda-gwani da ƙudirin ya ce za a riƙa yin ‘yar rinƙe, maimakon wakilan jam’iyya su riƙa yi.

Yayin da aka riƙa bayyana cewa wasu sanatoci sun fara rattaba hannun amincewa su yi amfani da ikon da doka ta ba su, su tirsasa kafa dokar, shi kuwa Femi Adesina cewa ya yi zai yi wahalar gaske su iya yin hakan, domin su na APC ne ke da rinjaye.

Adesina ya ce ai batun za su iya tirsasa dokar duk hauragiya ce, domin dai ba za su iya yin haka ɗin ba, kasancewar su jam’iyya ɗaya da Buhari.

Ya ce kamata ya yi tunda Buhari ya ƙi sa wa ƙudirin hannu domin ya zama doka, kamar yadda shi ma doka ta ba shi ƙarfin ikon yin hakan, to kamata ya yi sai a koma a yi maganar mene ne mafita? Ba wai a riƙa tsugunawa teburin mai shayi ana cewa majalisa za ta tirsasa kafa dokar ba.

Premium Times Hausa ta buga labarin cewa Sanatoci da Mambobin Tarayya za su yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe taron-dangi.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya ce sanatoci za su zauna tare da mambobin tarayya domin su samu mafita daga ƙin sa hannun da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2021.

Lawan ya bayyana haka a ranar Laraba a majalisa, kwana ɗaya bayan Shugaba Buhari ya aika masu da wasiƙar ƙin sa wa ƙudirin hannu.

Lawan ya ce a yanzu dai Majalisar Tarayya na hutu, sai watan Janairu za su koma aikin. Don haka da zaran an koma aiki, farkon abin da za su yi, shi ne zaman neman mafiya dangane da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.

Tun a ranar Talata Kakakin Majalisar Tarayya ya bayyana matakin da ya ce za su ɗauka tunda Shugaban Ƙasa ya ƙi sa wa dokar hannu.

Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya bayyana irin mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi amincewa ya sa wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Hannu.

A ranar Lahadi ce dai wa’adin kwana 30 su ka ya cika, domin Buhari ya sa wa dokar hannu ko ya ƙi.

Tun cikin watan Nuwamba aka aika masa da ƙudirin. Sai ranar Talata ce Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya cewa ba zai sa wa ƙudirin hannu ba, saboda batun zaɓen kai-tsaye na ‘yar-tinƙe.

Kakakin Majalisar Tarayya ya ce tunda hutun wata ɗaya za a tafi, Majalisar Tarayya za ta jira sai ta dawo daga hutu sannan ta ga abin da ya fi dacewa ga ƙasar nan.

“Ko ma dai me kenan, kada mu bari garin gyaran doro mu karya ƙugu. Ƙasar nan ce mafi muhimmanci a gare mu.”

A nasa bayanin, Shugaban Marasa Rinjaye Ndudi Elumelu, ya bada shawarar Majalisa ta gaggauta cire batun zaɓen-kai-tsaye a cikin ƙudirin gyaran zaɓen, sai a sake aika wa Buhari a ranar Talata ɗin kafin lokacin tashi aiki, yadda shi Buharin tilas ya sanya wa dokar hannu.

PREMIUM TIMES ta buga labarin iƙirarin da Sanata George Sekibo na PDP ya yi cewa, sama da Sanatoci 73 sun rattaba hannun kafa sabuwar dokar zaɓe ta hanyar bijire wa Buhari.

Sanata George Sekibo ya tabbatar da cewa akwai sama da sanatoci 73 waɗanda su ka sa hannun amincewa su tirsasa Shugaba Buhari su tabbatar da Sabuwar Dokar Zaɓe, wadda Buhari ya ƙi rattaba wa hannu domin ta zama doka.

Sekibo ya ce waɗanda suka rattaba hannun sun fito ne daga jam’iyyu daban-daban, kuma ana sa ran sake samun ƙarin wasu da dama.

Sekibo ya nuna damuwar sa a kan don me Buhari zai ƙi yarda a kafa dokar yin zaɓen-kai-tsaye na ‘yar-tinƙi a zaɓukan shugabannin jam’iyyu.

“Najeriya fa ba ƙasar mutum ɗaya ba ce, kuma ba wani kamfanin mutum ɗaya ba ne, ballantana ya ce sai abin da ya ga dama zai yi a kamfanin sa.

“Doka ta ba mu ikon kafa dokar, ko da Buhari bai amince ba, matsawar sanatoci da ke don a kafa ta sun kai kashi 2 bisa 3 na Sanatocin da ake da su 109.

“Sashe na 54 (4) da na 54 (5) ne ya bai wa sanatoci wannan ƙarfin ikon kafa dokar, duk da shugaban ƙasa bai yarda ba.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa wasiƙar yin fatali da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya wasiƙar sanar da su cewa bai yarda da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2021 ba, don haka ba zai sa wa dokar hannu ba.

Fatali da ƙudirin na ciki wasiƙar da Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya a ranar Talata ɗin nan, kuma majalisun biyu duk su ka karanta wasiƙun na shi a zaman ranar Talata ɗin nan.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne su ka karanta wasikar ga mambobin majalisar baki ɗaya.

Dama dai tun a ranar Juma’a ne 19 Ga Nuwamba, Majalisar Dattawa ta aika wa Buhari da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe ɗin.

A cikin doguwar wasiƙar da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya karanta, Buhari ya bayyana dalilan sa na ƙin sa wa ƙudirin hannu don ya zama doka.

Buhari ya ce ya karɓi shawarwari daga Ma’aikatun Tarayya, Ɓangarorin Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati.

Daga nan ya bayyana batun kuɗaɗe da batutuwan shari’u a matsayin dalilan sa na ƙin sa wa ƙudirin hannu.

“Idan aka yi wa dokokin zaɓen kwaskwarima, to karya karsashin dimokraɗiyya kenan. Wannan kuwa shi ne ‘yancin da kowace jam’iyya mutum ya ga dama ya shiga ya zama mamba.

“Sai dai kuma a shekara mai zuwa majalisa za ta iya zaɓen hanya mafita idan an dawo daga hutun ƙarshen shekara.

Makonni biyu da su ka gabata ne wannan jarida ta buga labarin cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta aika wa Fadar Shugaban Kasa wasiƙar amincewa da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar da batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.

Sai dai kuma INEC ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro, dangane da kudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙi jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara.

A ranar 29 Ga Nuwamba ce Majalisar Dattawa ta aika wa Shugaba Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka, ya na da kwanaki 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu, domin ya tabbata doka kenan.

Shi dai wannan sabon ƙudiri, matsawar Shugaba Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓen ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.

A cikin kwaskwarimar dai an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara.

Sai kuma batun suka sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga Buhari, kan batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe su ka ƙunsa.

Gambari ya shaida wa INEC cewa kada shawarwarin su wuce ranar 3 Ga Disamba.

Batun a koma yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen zaɓuka na fidda-gwanin takarar jam’iyyu ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da ‘yan majalisa waɗanda mafi rinjaye ‘yan APC ne, su da ɓangaren Bila Tinubu ke goyon bayan ‘yar-tinƙe, su kuma yawancin gwamnoni sun fi so a bar tsarin yadda ya ke, wato wakilai tun daga mazaɓu har zuwa sama su riƙa yin zaɓen fidda-gwani.