Wata Sabuwa: Gwamnatin Buhari ta rage girman aikin wutar Mambila daga 3,050MW zuwa 1,500MW

Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta ba da dalilin rage karfin aikin wutar Mambilla daga megawatts 3,500 zuwa megawatts 1,500, tana mai cewa ta yi hakan ne don tabbatar da isassun kuɗaɗe daga masu ba da bashi.

Jaridar This Day ta ruwaito Ministan Wutar Lantarki, Salleh Mamman, wanda ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai kan wutar lantarkin ya ce an mayar da karfin aikin wutar zuwa megawatts 1500 domin sanya shi a matsayin mai sauki da karbuwa ga masu ba da bashi.

Ya ce: “Mun gano cewa megawatts 3,050 ba zai iya samuwa ba. Mun tura jami’ai zuwa China don duba aikin kuma takardar tana shugaban kasa muna jiran amincewar sa.

“Tunanin sake fasalin aikin shi ne don a samu nasara. Darajar chanjin Dala da muke aiki da ita a yau a Najeriya ta bambanta da take a kasuwar da muke aiki da ita lokacin da aka ɗauki aikin Mambilla.

“A yau muna buƙatar wani aiki wanda za a iya biyan sa a sawwaƙe. Muna tallafawa aikin tare da bashi daga ma masu ba da bashi wanɗa kawai ke sha’awar ba da bashi ga aiki wanda zai iya mayar da bashin”. A cewar Ministan.

A nasa jawabin, Shugaban kwamitin, Sanata Gabriel Suswam, ya nemi Ministan da ya yi bayani a kan Naira miliyan 812 da gwamnatin tarayya ta biya gwamnatin jihar ta Taraba domin yin nazari da share filayen da za a kafa aikin.

Suswan ya ce dole ne ma’aikatar ta yi bayanin yadda aka yi amfani da kudin tunda gwamnatin tarayya ta bayar inda ya kara da cewa “ya rage gare ku ka nemi gwamnatin Taraba ta kawo maka cikakken bayanin yadda aka kashe N812 miliyan”.

Da yake mayar da martani, Ministan ya ce an biya kudin ne ga gwamnatin jihar Taraba bisa yarjejeniyar da aka yi tsakanin jihar da gwamnatin tarayya.

Kamfanin samar da wutar lantarki na Mambilla wanda ya kai dala biliyan 5.8 a jihar Taraba da aka tsara sama da shekaru talatin da suka gabata, an tsara shi ne don samar da wutar lantarki megawatt 3,050.

A shekarar 2017, gwamnatin tarayya ta amince da gina wannan aikin ga wani kamfanin kasar Sin.

Bankin shige da ficen kayayyaki na ƙasar Sin ne ya amince zai samar da kashi 85 na kuɗaɗen yin wannan aiki sannan gwamnatin Najeriya ta samar da sauran kaso 15 na haɗin gwiwar.