Majalisar Katsina za ta maida gidajen kallo makarantun Islamiyya

A ranar Talata ne ƴan majalisan dokokin jihar Katsina suka tattauna yiwuwar maida duka wuraren kallo da gwamnati ta gina a kauyuka da garuruwan jihar zuwa makarantun Islamiyya.

Ɗan majalisan dake wakiltan karamar hukumar Jibia ne ya jagoranci muhawarar a zauren Majalisar jihar.

” Lokaci yayi da za a maida gidajen kallon Talbijin da aka giggina a kauyukan su koma makarantun Islamiyya domin sune ake bukata yanzu ba wuraren kalle-kalle ba.

” Na yi hira da wasu ƴan bindiga kuma koken da suka yi min kenan na rashin makarantu da suke fama da su. Sannan kuma su kansu wuraren kallo da yawa daga cikin su sun zama kufayi, sun lalace.

” Idan majalisa ta amince da wannan kudirin za a samu saukin Almajirai dake gararamba a jihar sannan kuma za a ɗibi malamai wanda zasu rika karantar da yara, shima hakan hanyar samar da aikin yi ne.

” Tarbiyya ya tabarbare saboda rashin ilimin addini da yayi karanci wa yara. Wannan zai sa su san addinin su sannan sukuma ilmantu.

Wasu daga cikin gidaden kallon sun zama matattaran ƴan iska

A karshe kakakin majalisar Tasi’u Maigari ya mika kudirin ga kwamitin addini domin su duba sannan su baiwa majalisar shawara kan abinda ya kamata suyi.

Jihar Katsina, kamar wasu jihohin Arewa Maso Yamma, na fama da tsananin rashin tsaro.

Hare-haren ƴan bindiga yayi tsanani sace yaran makaranta.