Babban hafsin sojin ƙasa Faruk Yahaya ya zama Laftanar Janar

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a yau Laraba tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo sun maƙalawa sabon shugaban hafsan tsaro na ƙasa Faruk Yahaya shaidar ƙarin matsayi daga Manjo Janar zuwa Laftanal Janar.

Buhari ya jagoranci ɗan taƙaitaccen bikin ne kafin soma taron majalisar zartaswa ta ƙasa da aka saba jagoranta a duk ranar Laraba.

A ranar 27 ga watan Mayu, 2021 ne shugaban ƙasa ya naɗa Laftanar Janar Faruk Yahaya shugaban hafsoshin sojojin ƙasa wanda ya maye gurbin Marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama a Kaduna.