Wani sako da ake yadawa wai a aika da harafin “W” zuwa 50017 don samun kudi kyauta zamba ce – Binciken DUBAWA

Zargi: Akwai wani sakon da ake samu a wayoyin hannu wanda ke nuna wai Gwamnatin Tarayya ta fara baiwa wasu ‘yan Najeriya 200, 000 kyautar kudi.

A watan Agusta na 2021 gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa akai shiri da take yi na fara baiwa mutane 200,000 kudi. Wannan himma zai hada da dattawan da ba a biyan su albashi ko kuma basu da hanyar samun kudaden shiga akai–akai wadanda tsananin matsi na rayuwa yayi wa tsanani a dalilin annobar COVID-19.

To sai dai kusan watanni biyu da wannan sanarwa, wani sako ya fara yawo a wayoyin jama’a yana cewa wai gwamnatin tarayya za ta sake fara aikawa mutane ‘yan Najeriya 200,000 kudi kyauta.

“KINS# Gwamnatin Tarayya ta fara tura kudi zuwa ‘yan Najeriya 200,000 daga jihar Legas zuwa Imo da sauran jihohi 36. Allah sarki Najeriya. Idan har ba ku samu ba, ku tura “W” zuwa 50017 dan samun karin bayani”

Duk da cewa ba sabon labari ba ne wai gwamnati na yin abu makamancin wannan, masu zamba na amfani da wannan damar su yaudari mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Tantancewa

Da farko Dubawa ta bi diddigin sakon inda ta gano cewa “W” “50017” hanyar shiga dandalin aikawa da sakonnin da aka fi sani ne da “Mblog” Kamfanin SICS ne ya kirkiro Mblog tare da tallafin kamfanin Ericsson dan kwastamomin da ke amfani da layin MTN.

Idan har mutum ya tura “W” zuwa “50017”, kai tsaye zai shiga wani dandalin tattaunawa daga nan zai bi wasu umurnin da sukan tanadi zabar sunan da zai yi amfani da shi a dandalin. Bayan sun sami sakonni dangane da kyautar kudin, za su sake samun wadansu sakonnin da ke cewa su gayyaci abokansu zuwa dandalin dan su gwada amfani da shi a kyauta.

Sadda Dubawa ta tattauna da wakiliyar MTN, Madam Elizabeth, ta amince cewa akwai Mblog amma ta ce ko daya ba ta san batun da ya shafi kyautar kudin ba har ma ta gargadi jama’a su yi hattara.

“Masu amfani da layin MTN na iya shiga Mblog amma batun wani tura “W” zuwa “50017” dan samun kudi ba ni da wannan labari, shawara ta ita ce jama’a su yi watsi da wannan sako.” Inji Elizabeth

Ta kuma kara da cewa, “ idan MTN ne ta fidda wannan sako, da ta yi cikakken sanarwa a kai ba ta yadda aka rika yadawa ba. Ba bu abinda ya hada MTNwannan sako.

A karshe

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta baiwa wasu kudade a baya sakon da ke yawo yanzu karya ne kuma ba shi da alaka da Gwamnatin Tarayya.