Ƴadda ƴan bindiga suka kai wa jirgin ƙasan Abuja-Kaduna hari da bama-bamai

Matafiya sun faɗa cikin tashin hankali bayan ƴan bindiga sun kai wa jirgin ƙasa hari da bama-bamai

A ranar Alhamis ne matafiya da ke hanyar su ta zuwa babbar birnin tarayya, Abuja daga Kaduna suka afka cikin halin ha’ulai, fargaba da tashin hankali bayan ƴan bindiga sun kai wa jirgin kasan hari da bama-bamai.

Cikin matafiyan da abin ya auku a idon su kuma tsohon sanata dake wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa Allah ne ya kubutar da su daga wannan hari, domin maharan sun ɗan bam a layi dogon inda ya dagargaza layin.

” Sai dai kuma Allah ya sa jirgin ya wuce wannan wuri ba tare da ya kife ba. Matafiya sun isa Abuja duk da haka.

Wannan mummunar abu ya auku ne tsakani Rujana da Dutse.

Sai dai kuma ba Ranar Alhamis bane maharan suka kai harin farko, an ce sun bude wa jirgin wuta ranar Laraba da dare, wanda yasa dole sai da ya tsaya.

Maharan sun buɗe wa jirgin kasan wuta a daren Laraba.