ALAMOMIN TARWATSEWAR APC A KANO: Tsakanin Ɗanzago Da Ɗan Sarki’, Wane Ne Ɗan-yaga-rigar Jam’iyya?

An yi mamakin yadda rikici ya kunno kai a cikin jam’iyyar APC a Jihar Kano, tun kafin zaɓen ‘yan takarar gwamna a zaɓen 2023 mai zuwa.

Amma kuwa dama kowa ya san akwai rashin jituwa sosai a cikin APCin Kano, ganin sai yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya ga dama ya ke yi.

Zaɓen shugabannin jam’iyya da aka gudanar a makon jiya ya farraƙa jam’iyyar gida biyu, wato ɓangaren Gwamna Ganduje, waɗanda su ka sake zaɓen Abdullahi Abbas a matsayin shugaba. Sai kuma ɓangaren su Sanata Ibrahim Shekarau, waɗanda su ka zaɓi Haruna Ɗanzago a matsayin na su shugaban.

Yayin da a wata sanarwar da APC ta ƙasa ta yi, ta bakin Salisu Na’inna Ɗambatta ta ce ɓangaren Ganduje ne halastattun shugabanni, shi kuma Sanata Ibrahim Shekarau ya ce ba za su bi waccan gayyar shugabancin su Abdullahi Abbas ba.

Dama ita APC a Jihar Kano kusan ɓangaren ‘yan gidan siyasa biyu ne su ka cika ta. Ɓangare na ɗaya shi ne mutanen da su ka ‘ci amanar’ tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso, sai kuma irin su Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna, ‘yan gidan siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, wanda shi ma ya yi gwamna sau biyu kamar yadda Kwankwaso ya yi.

Abin tambaya, tunda kowa ya ja ta sa gayyar, wa ku ke ganin zai fi jan ɗimbin magoya baya?

Kuma idan ɗaurin tsintsiyar ya ƙarasa tarwatsewa, shin tsakanin Ɗanzago da Abdullahi Abbas (Ɗan Sarki), wane ɗan-yaga-rigar da ya kekketa zanin APC?