TSIGE MALA BUNI: Umarnin Buhari muka bi, dama kuma jam’iyyar APC na cikin halin rudani a karkashin sa – El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnoni 19 na jam’iyyar APC suka amince da tsige gwamman Yobe Mala Buni daga kujerar shugabacin jam’iyyar APC na riko.

” Duk wani gwamna da ya fadi wani abu da ba haka ba, ku rabu da shi zuki ta malli ne, wai har ana cewa idan ya dawo daga tafiyar sa zai cigaba da rike jam’iyyar APC. Wannan ba gaskiya bane. An riga da an tsige shi daga wannan kujera.

El-Rufai ya kara da cewa Buhari ne ya basu umarnin a kauda Mala Buni daga wannan kujera na shugabancin jam;iyyar APC kuma gabadayan su sun amince da hakan tuni ma har gwamnan Neja, Sani Bello ya dare kujerar riko na jam’iyyar.

” A baya wasun mu sun koma da baya ne sun kyale jam’iyyar a hannun wasu domin su kula da ita, amma kuma da ga baya sai muka gano lallai suna neman su jefa ta cikin rudanin da ba za a iya ceto ta ba. Dalilin haka ne ya sa dole ire-iren mu masu kishin jam’iyyar muka yunkuro domin ceto ta daga hannu wadannan mutane.

” Dukkan mu 19 mun gana da shugaba Buhari kuma ya amince mana mu je mu yi abinda ya dace a yi. kafin ya dare jirgi.

Sai dai kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya shaida wa wasu magoya bayan jam’iyyar cewa, Mala Buni ne shugaban jam’iyyar har yanzu. Da kansa ya amince Bello Sani gwamnan Neja ya rike masa kujerar kafin ya dawo daga Dubai.

Amma kuma El-Rufai ya ce duk rudu ne, aikin gama ya gama.