TASHIN HANKALI: Sojoji 18 ‘yan bindiga suka kashe a Kanya jihar Kebbi – Rundunar Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojoji 18 da ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Kanya, jihar Kebbi.

A wani harin kare dangi da ‘yan bindiga suka kai wa tawagar mataimakin gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe, a Kanya dake karamar hukumar Dangu Wasagu sun hallak jami’an tsaro 19 dake tare da tawagar mataimakin gwamnan.

Wani mazaunin garin Kanya Labaran Magaji ya bayyana cewa tun wajen misalin karfe 5 na yamma ne ‘yan bindigan suka dira kauyen Kanya suka yi ta batakashi da jami’an tsaron da ke tare da mataimakin gwamnan.

” Allah ne kawai ya tsirar da mataimakin gwamna Yombe domin a wannan hari sun nemi sai sun kashe shi ne amma Allah ya tsirar da shi.

” Sai dai kash, maharan sun kashe jami’an tsaro da dama ciki har da sojoji 13 da yan sanda 6. Zuwan wasu sojojin ne ya sa ‘yan bindigan suka arce daga nan sai suka kwashe gawarwakin ‘yan uwansu da aka kashe.

Wani mazaunin yankin Ahmed Umar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa mataimakin gwamna Yombe ya kai ziyarar jaje ne ga iyalai da ‘yan uwan yan bangan da mahara suka kashe a harin kwantar bauna a Sakaba kwanaki biyu da suka wuce.

A can garin Kanya mahara suka afka masa har Allah dai ya sa shi ya tsira amma kuma jami’an dake tare da shi har 19 suka yi sallama da duniya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su zage damtse wajen gamawa da ‘yan bindiga dake kai hare-hare a yankin jihar Kebbi bayan kisan ‘yan banga 63 da mahara suka yi.

A sanarwar da rundunar ta fitar ranar Alhamis ta ce bayan batakashi da sojojin suka yi da ‘yan bindigan sun kashe dakaru 18 sannan sojoji biyu sun bace.