DABARUN TANADIN KAYAN NOMA: Najeriya ta hana ‘yan ƙasar waje sayen kayan gona kai-tsaye daga hannun manoma

Gwamnatin Najeriya ta hana baƙi ‘yan ƙasar waje sayen kayan gona kai-tsaye daga hannun manoman mu a cikin gida.

A ranar Laraba ce dai gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar a shafin ta na Tiwita, inda ta yi ƙarin haske da cewa ejan-ejan ne masu cikakkar ragista ne aka amince su riƙa sayen kayan gona daga hannun manoma.

“A yau Gwamnatin Tarayya ta amince da haramta wa duk wani baƙo ɗan wata ƙasa zuwa sayen amfanin gona daga hannun manoman ƙasar nan.

“Saboda haka sai dai ejan-ejan ne masu lasisi za su riƙa saye daga hannun manoman cikin Najeriya.”

Ministan Cinikakkya, Kasuwanci da Zuba Biyu Adebayo ne ya bayyana cewa ana samun rahotannin yadda baƙin haure ke zuwa har cikin gonaki a wurin manoma su na yi masu dabarar sayen kayan gonar su a farashi mai arha takyaf.

Ya ce irin haka da ake yi wa manoman ya na kashe masu guiwar fitar da kayan su domin su ci riba.

Ya ce Ministan Shari’a, kuma Antoni Janar Abubakar Malami zai tsara ƙudirin da za a aika Majalisar Tarayya ta duba kuma ta rattaba masa hannun amincewa ya zama doka.”

Da ya ke jawabi, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (RIFAN), Ibrahim Kabir ya ce wannan mataki da Ma’aikatar Cinikakkya ta bijiro da shi.

Yayin da Shugaban RIFAN ya goyi bayan wannan sabon mataki da Gwamnatin Tarayya ta bijiro kan manoma, wasu kuma sun fara kukan cewa tsarin wani bahago ne, kuma zai dagula yanayin kasuwancin amfanin noma.

Sun bada shawarar cewa bai kamata a hana baƙi sayen tun daga gona, kawai a bari kowane amfanin gona ya sayar da kan sa.