TSADAR GAS: Masu siyar da Itace da gawayin girki na caba ciniki a Najeriya

Tsadar iskar gas ya sa kakan masu siyar da itace da gawayi ta yanke saka ganin yadda mutane suka koma girki da itace ko gawayi a kasar nan.

A yankin Kudancin kasar nan masu siyar da itace ko gawayi sun bayyana cewa tun a watan Satumba da farashin gas ya tashi suke samun ciniki.

Sakamakon binciken da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta gudanar a kudancin kasar nan ya nuna cewa kg1 na iskar gas da ake siyar da shi akan Naira 700 ya koma 900 kuma 12.5kg ya koma Naira 11,250.

A Calaba jihar Cross Rivers Mrs Eno Akan ta ce yanzu ta koma amfani da itace gon girki saboda tsadar farashin iskar gas.

Wani mai siyar da itace a kasuwan ‘Beach’ Samuel Bassey ya ce shi dai kakansa ta yanke saka a sana’ar sa na siyar da itace.

Bassey ya ce yanzu mafi yawan mutane da gidajen siyar da abinci na zuwa wajen sa siyan itace.

“A yanzu haka Ina sauri ne na kai itace dauri 50 wani gidan abinci da suka yi oda a hannu na.

Ita ko Theresa Odum ta ce duk da tashin farashin gas ta gwamace girka abincin ta da gas.

“Girki da itace na da wahala, ga hayaki, ga dadewa wajen girki sannan ga bata wuri da baki.

Shugaban kula da gandun daji na ma’aikatar muhalli na jihar David Egbe ya ce mutane na ta sare itatuwa a jihar duk da dokar hana yin haka da gwamnati ta saka.

Wani Mai kula da muhalli James Okon ya ce yin girki da itace na cutar da lafiyar mutane.

“Girka abinci da itace na haddasa cututtuka kamar su hawan jini, ciwon asthma, tarin fuka, dajin dake kama huhu da makamantan su.

A garin Fatakwal Margret Ephraim ta ce rashin samun wutan lantarki, tsadan kudin lantarki na cikin dalilan dake sa mutane yin amfani da gawayi wajen girki.

“Idan ana samun wutan lantarki da gas da arha girki da itace ko gawayi zai zama tsohon yayi.