El-Rufai ya yagalgala APC a Kaduna, cikin ruwan sanyi PDP za ta yi wuf da Kaduna a 2023 – Mr LA

Jigo a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna Lawal Usman da aka fi sani da Mr LA ya ce jam’iyyar PDP za ta karbi Kaduna cikin ruwan sanyi ne daga hannun APC a 2023.

” Gwamnan Kaduna Nasir El=Rufai yayi ragaraga da APC a jihar Kaduna. Mutanen Kaduna ba za su manta da wutan da ya gasa musu a hannu ba.

Mr LA ya bayyana haka a gari Zariya ranar Lahadi a lokacin da yake hira kamfanin dillancin labarai.

” Aikin Sabunta Kaduna ya saka mutane da dama cikin yanayi na kunci da talauci. Wasu sun rasa gidadjen su da dukiyoyin su. Babau yadda za a gina gari ba tare da an gina mutanen gari ba. Suna tafiya ne hannu da Hannu.

Mr LA ya ce mutanen Kaduna sun gaji da wannan tsari na El-Rufai, wahalar ta yi yawa, neman mafita kawai su ke yi yanzu, kuma mafitar ita ce PDP.

” Gina gari na da mahimmanci amma kuma dole a rika sara a na duban bakin gatari saboda, mutanen da za su ci moriyar aikin suma a duba su.

Idan ba kana so mutane su rikide su zama barayi ko yan tada zaune tsaye bane, ba za ka rusa musu wuraren zaman su baka basu wani wurin ba ka ce za a zauna lafiya. tsananin yayi tsanani a Kaduna.

Ko shakka babu jihar Kaduna ta PDP ce a 2023, bana haufi ko tantama. Masu so a dama da su suna dawowa daya bayan daya.